Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Zarif yana fadar haka a yau asabar a wani taro, dangane da makomar kungiyar ta Daesh da aka gudanar a jami'ar Tehran.
Zarif ya kara da cewa banda haka, akidar da ta samar da Daesh tana nan a yankin, kuma kasashen da suke goyon bayanta, suke kuma bata kudade suna ci gaba da tallafa mata, don haka akwai yiyuwan kungiyar ta sake bulluwa a ko wani lokaci.
Mohammada Jawada Zareef ya ce Amurka ta yi jigilar mayakan kungiyar Daesh daga yankunan Hasaka, Dair-Zur da sauran wurare a kasar Siria da Iraqi zuwa wasu kasashen don tayi amfani da su a duk lokacinda ta ga dama.